Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na biyar

Menene hukuncin masu biyan wasu su rubuta masu jarabawar gaba da sakandare?
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Manene hukuncin shiga aikin soja, musamman a wannan lokacin?
Daga Kabeer M Nazeer Samaru Zariya jihar Kaduna.
Malam Kabeer in ka duba a ALMIZAN na baya za ka ga amsar irin wannan tambayar, domin mun taba buga irinta.-Edita
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko sanya wata da tauraro da musulmi suke yi a masallaci yana da asali?
Daga Kabeer M Nazeer Samaru Zariya jihar Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: Ba za mu ce ba shi da asali ba, kuma ba za mu ce yana da asali ba, wato mu ce yana da matsayi a shari'a wanda ta ce a yi ba. Sai dai wani abu ne wanda yake a tarihi a kan cewa mayaka sukan kasance suna da alamomi wanda yake bambanta su daga sauran, wanda sukan sa a tutocin su. Wannan wani abu ne ma'alumi adatan. Kuma a lokacin Annabi ma an yi amfani da irin wannan. Wanda aka ce ma a tutar Manzon Allah akwai mikiya. Kuma wani lokacin da aka yi yakin Afranj, Faranjawa, wadanda ake ce wa 'Crusaders' kenan, sukan zo da alamomin sakandami a tutocinsu. A wannan lokacin sai ya zama su ma Musulmi sukan sa wata da tauraro a tutocinsu. Haka kuma dauloli da daman gaske sun yi amfani da irin wannan, har yau da kullum ya zama wani abu wanda ake alamta al'ummar musulmi da shi.
Wato ba za mu ce ba shi da asali ba, ba kuma za mu ce yana da asali a shari'a ba. Sai dai a shari'a, duk abin da ba a hana ka ba kana iya yi. An san akan yi alami na mayaka ko ta al'umma, kuma babu laifi idan ku mayakan musulmi ko kuma al'ummar musulmi suka dauki alami, kamar wanda suka ga yana da dangantaka da addininsu, suka sa shi a matsayin alamarsu. Kamar tauraro, masalan, ko kuma da jaririn wata wanda yake al'ummar musulmi suna ba jaririn wata muhimmanci saboda ayyukan ibadodinsu na azumi da Hajji da sauransu. To in suka dauko shi suka ce saboda wannan ya alamta wani abu nasu, ba wani laifi da shi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Menene hukuncin tsai da haihuwa da wasu ke yi da umurnin Likita ko ba da umurninsa ba?
Daga Abu Ramlat Samaru Zariya jihar Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: In dai ba da azalu ne ko kuma kaurace ma mace a lokacin da ba a bukatar ta dauki ciki ba, wato wanda za a yi yarjejeniya tsakanin mata da miji ba, wanda yake shi an san shi, wadansu hanyoyi da yanzu ake amfani da su, sun nuna tamkar zubar da ciki ne da wayo. Domin ya tabbata cewa magungunan da mutane suke sha na maganin hana daukar ciki, ashe ba yana hana daukar ciki bane, yana tarwaatsa cikin ne in ya dauku. Ko dai a lokacin da kwan ya sami matsattsakun namiji a kan bututun nan nasu da ya fito, kafin ya kai ga mahaifa sai ya tarwatse, don shi wannan maganin zai hana shi zuwa ga wurin, ko kuma in ya je mahaifar, zai zama ba zai iya mannuwa da mahaifar ta yadda zai zama da ba, sai ya dagwargwaje ya zube. Ka ga tamkar zubar da ciki ne ta wata fuska, tun yana dan karami. Saboda haka idan mutane suka dauki matakin da shari'a ta sani, kamar irin na azalu da kauracewa domin gudun kar a dauki ciki a wani lokacin da ake tsammanin za a dauka. Za mu iya cewa ba laifi da shi, in tsakanin ma'aura biyu suka yi yarjejeniya, hakkin miji ne hakkin mata ne, sai sun yarda dukkansu. Da shawarar Likita ko ba da shawarar Likita ba. Amma idan ana batun kamar in ta dauki ciki, zai kai ta ga mutuwa ne, masalan, ta inda ba zai yiwu ta yi ciki ta haihu ba tare da ta mutu ba, to wannan sai ya zama hana daukar cikin zai zama ya halasta, ko ma ya wajaba.
TAMBAYA: Akramakallahu. Dangane da wankan janaba na mata, wasu matan sukan kitse kansu yadda ruwa ba ya shiga ko'ina a kan nasu. Wasu kuma suna shafa ruwa kawai a kansu sai su ce ya wadatar da su. Shin wankan nasu ya inganta kuwa?
Daga Muhammad Garba Kankiya jihar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani shi ne cewa duk jiki sai ya sami ruwa a wajen wanka, ruwan kuma ya wanke shi da ma'anar wankewa, wato ya gudana a jikinsa kenan har ya zube. Kuma gashi yana daga cikin bangaren jikin mutum. Saboda haka ko silin gashi daya in bai sami ruwa ba da sunan ya wanke shi a wanka ba, to janaba tana nan. Saboda haka lazim ne mace ta tabbatar da cewa dukkan gashinta ya sami ruwa da sunan wanki, ba wai an shafa masa ba, an wanke shi da ruwa. Batun kitso kuwa, idan kitson zai hana ruwan ya shiga ya wanke gashin, to zai zama wajibi ne a warware shi. Amma idan ko yana daure, ruwa zai iya wanke shi ya tabbata kuma ya wanku. Ba batun kitson muke magana ba, batun wanke gashin muke magana. Saboda haka in dai gashin ya wanku, to ya wadatar. Ka ga abin da yake wajibi shi ne wake gashin ta kowane hali, kamar sauran abin da bayyana zahiran a jikin mutum a wajen wankan janaba, dole ya wanke shi.
TAMBAYA: Akramakallahu.Uba ne da dansa suna tafiya a mota sai suka yi hadari duk suka mutu, amma ba a san wanda ya riga wani mutuwa ba daga cikinsu. To wa zai ci gadon wani?
Daga Muhammad Garba Kankiya jihar Katsina
MALAM ZAKZAKY: Duk cikarsu za su gaji juna ne, uba zai gaji da, da zai gaji uba. Sai a fara rabon gadon uba, sai a cire wa da kasonsa, sannan bayan kuma an gama sai a raba gadon da a cire wa uba kasonsa. Sai sauran magadan uba su sake gadon abin da ya gada daga dansa. Magadan da kuma su gaji abin da da ya gada daga wajen ubansa.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Yaya matsayin wanda ya ba maroka kudi a gidan suna ko biki?
Daga Muhammad Garba Kankiya jihar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Ba a ce ba a ba maroka kudi ba, a suna ne ko a biki ko ba a ko daya ba. Sai da ba a karfafa gwiwar ba su da yawa, ana cewa a ba su kadan ne don a tsira daga sharrinsu.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan wani zai roki wani abu a wajen wani nakan ji yana cewa "don Zatin Babanka." Yaya halascin yin wannan abu yake a Musulunci?
Daga Abdullahi Sani Jushi Zariya jihar Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: To shi dai in ya zo da unwanin sadaka ne, ana yin sadaka domin Allah ne. In yana nufin don wanene ya ba da? To sai ya zama dole zai bayar domin Allah ne. Amma gamar da mutum ya yi wani aiki na alhairi da darajar wani, ba yana nufin wannan aikin an yi wa wannan din ne ba. Ana iya ce maka albarkacin wane ka yi kaza, amma in ka yi din ba yana nufin wane din ka yi wa ibada ba, sai dai in ya yi da nufin shi wannan ibada ne, to shi ne zai zama tamkar ya bauta masa kenan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan mutum ya sami sabani da matarsa, sai ta ce ya sake ta, to wane mataki zai dauka?
Daga Abdullahi Sani Jushi Zariya jihar Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: To akwai matakai da aka ba miji da mata shawarar yadda za su dauka don warware matsaloli. Kamar wa'azi, wa'azin bai yiwu ba, an kaurace kauracewar ma bai yiwu ba. Sannan sai kai abin gaba ga wadansu wadanda za su sasanta tsakanin miji da mata din. Sai su su duba su ga ina za su iya sa yabo, ina ne za su sa laifi da kuma mene za su yi ya zama maslaha a tsakaninsu? Amma ba saki ne kawai aka sani yake warware maganar aure ba.
TAMBAYA: Akramakallahu. Zan iya yi wa Mahaifina layya duk shekara, duk da cewa ya rasu?
Daga Aminu Mai faci Kanhawa,Tudun Wada Funtuwa jihar Katsina
SHAIKH ZAKZKY: A'a, ba za ka iya masa layya ba. Ta fuska guda zai yiwu ka yi, shi ne inda dama ya yi tanajin rago zai yi layya din sai Allah ya yi masa rasuwa, to za a iya a yi masa layya din. Ko kuma an ji ya furta cewa yana da niyyar ya yi, to shi ma ana iya yi masa, amma banda sauran shekaru kuma da suka biyo baya, ba zai yiwu ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halasta musulmi ya ba da zakka ga wanda ba musulmi ba?
Daga Aminu Mai faci Kanhawa,Tudun Wada Funtuwa jihar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Eh! Ta fuskacin jawo hankalinsa ya shiga Musulunci. Shi ne wanda a nassin Alkur'ani ana ce masa "Mu'allafati kulubuhum" wato wanda ake jan hankalinsu, ana iya ba su zakka. Ta wannan unwanin kawai. Wato ta fuskacin jawo hankalinsa ya ga kyawun Musulunci, da fatan ya musulunta. Amma in ba ta wannan fuskar ba, mujarradin kawai a ba shi ne kawai, to ba zai halatta ba.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Meye hukuncin masu biyan wasu suna rubuta masu jarabawar gaba da sakandare, don su sun manta da karatun saboda sun wuce wannan 'level' din?
Daga Husain Abdullahi, Dept of Biological Science BUK
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba zai halatta ba, saboda wannan ya zama tamkar yaudara kenan. In dai har za a ba ka takardar shaida cewa ka ci jarabawa, to wanda duk ya ga takardar, abin da ya fahimta shi ne kai ka rubuta jarabawar ka ci. Saboda haka in har ma za a ba ka aiki bisa la'akari da cewa wannan kai ka rubuta jabawar ka ci, saboda haka nan ne ma aka dauka ka iya aikin aka ba ka, aka kuma biya ka lada. Saboda haka in ka sami wannan aikin da takardar shaida ta jabu, to zai zama abin da ake ba ka ma zai yiwu ya haramta maka. Wannan kamar cin amana ne.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halasta musulmi ya sayi bidiyo da talabijin don ya rika kallo?
Daga Aminu Mai faci Kanhawa,Tudun Wada Funtuwa jihar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Kallo dai, mujarradin kallo, ba shi ne zai zama haramun ba, amma a cikin abubuwan da ake kallo din akwai haram da halas. Saboda haka abin da ya halatta ka kalla ne kawai za ka kalla. Kuma abin da ya haramta ka kalla ba za ka kalla ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan wanda ba musulmi ba ya yi wa musulmi sallama, wace amsa zai ba shi?
Daga Ibrahim Limanci Dala Kano
SHAIKH ZAKZAKY: To masana fikihu suna cewa ya ba shi amsa wadda shi zai gamsu dai an ba shi amsa, amma ba irin wadda zai yi wa dan uwansa musulmi ba. Alal misali, ba zai ce "wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu" ba. Sai ya yi masa raddi da 'alaikum' ko 'wa alaikum'ko kuma wata kalma mai ma'ana, kamar 'yawwa, madalla, eh, muna lafiya ko barka ka dai,' da abin da ya yi kama da haka nan.
TAMBAYA: Akramakallahu. Na ji ana cewa duk mutumin kauye ba zai yi hankali ba sai ya shekara 40. Shin wannan gaskiya ne?
Daga Ibrahim Limanci Dala Kano
SHAIKH ZAKZAKY: Eh! To hankali dai ba shi da dangantaka da kauye ko birni, akwai mara hankali a kauye akwai mara hankali a birni. Amma dai abin da muka sani shi ne, kamalar mutum, na kauye ne ko na birni, shi ne cika shekara 40. Kamalar mutum namiji sai ya shekara 40, mace kuma shekara 33. Saboda haka dan shekara 40 ana daukarsa a matsayin dattijo.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. 'Yan uwa ne suke zaune su biyu a gida guda kowanne da matarsa. Shin ya halasta dayan ya jagoranci matan salla ko da daya maigidan ba ya nan?
Daga Ibrahim Limanci Dala Kano.
SHAIKH ZAKZAKY: Mu dai abin da muka sani shi ne salla dai akan yi jam'i, kuma jam'in nan yakan zama akwai liman da sahun maza sannan sahun mata, amma ba wani wanda yake tambayar dangantaka ta auratayya tsakanin Liman da wadda take bin salla. Sau da yawa ma shi Liman bai san su waye suke bin shi salla ba. Abin dai da aka sani shi ne sahun maza sannan sahun mata. Su matan nan ba su da wani dangantaka ta zumunci ko ta auratayya da su da liman. Kuma ma bai san suna bin sa salla ba ma, bai ma san su ba. Ba a ma ce sai ya san su ba. Sune ma yake lazim su yi niyyar ibtida'i, ba shi ne yake niyyar zai jagorance su kan salla ba, in ba dai na Juma'a bane.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ko dan uwa zai iya shiga dakin matar wani dan uwa yana nan ko ba yana nan tunda tana sa hijabi, saboda kusanci da shakuwar da suke da juna (su 'yan uwan)?
Daga Muhammad Ibrahim Lawan Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: Abin da aka sani shi ne ya haramta mutum ya kadaita da wata mata 'ajnaba,' wato wadda take ba matarsa ba ba kuma muharramarsa ba a dakin da ba zai yiwu a gan su ba ko da kuwa labule ne ya rufe, ko ma daji ne, falalen dajin da ba zai yiwu a gan su ba. Ala ayyi halin, kadaici da matar da ba matarsa ta aure ba, ba muharrama ba, ya haramta. Kadaicin kuma yana nufin ya zama ba a ganin su. Saboda haka in dai za su kadaita ba zai yiwu a gan su ba, zai haramta. Ko da kuwa tana sanye da hijabi.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved